An yi cacar-baki tsakanin Donald Trump da Zelensky

Facebook Twitter LinkedIn
An yi cacar-baki tsakanin Donald Trump da Zelensky

Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya bayyana a fusace ya kara da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, a ziyarar da shugaban na Ukraine ya kai Amurka ranar Juma'a.

A lokacin cacar-bakin da ta kaure tsakanin ɓangarorin biyu, Trump ya shaida wa Zelensy cewa ya cimma yarjejeniya da Rasha ko muka "mu rabu da kai".

Mutanen biyu sun riƙa katse juna a lokacin zazzafar cacar-bakin, wani abu da ba a saba gani ba a fadar shugaban ta Amurka.

A tsakiyar cacar-bakin, Trump ce Zelensky bai gode wa Amurka kan tallafin kayan yaƙi da na siyasa da ta ba shi ba, kuma yana caca da "yaƙin duniya na uku."

A ɗaya ɓangaren Zelensky ya ce bai kamata a "ɗaga ƙafa" ga shugaban Rasha, Vladimir Putin ba.

Sai dai Trump ya ce wajibi ne Ukraine ta nuna sadaukarwa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha.

An tsara yin ganawar ce ta kasance gabanin sanya hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adanai da ɓangarorin biyu za su sanya wa hannu, wadda a ƙarshe ba ta gudana ba.

A wani lamari mai kama da kwance wa Zelensky zani a kasuwa da Trump da mataimakinsa JD Vance suka yi, mataimakin shugaban na Amurka ya fara da sanar da Zelensky cewa wajibi ne a kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar diflomasiyya.

Zelensky ya mayar da martani da tambayar "wace irin diflomasiyya?"

Daga nan ne kuma JD Vance ya zargi Zelensky da kasancewa maras girmama mutane.

Daga nan ne abubuwa suka ci gaba da dagulewa, inda Trump da mataimakinsa Vance suka zargi shugaban Ukraine da rashin gode wa Amurka a tsawon shekara uku na yaƙin, duk da taimakon da ta bai wa ƙasarshi.

Trump ya gargaɗi Zelensky kan cewa ba shi ne ya kamata ya faɗa wa Amurka abin da za ta ji ba.

Jim kaɗan bayan taron, ba tare da an kammala sauran abubuwan da aka tsara ba, an ga Zelensky ya fice daga fadar White House a motar da ya zo.

Haka nan kuma jim kaɗan bayan hakan Donald Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa "Zelensky ya yi wa Amurka rashin kunya a ofishin shugaban ƙasa mai martaba".

Ya ƙara da cewa "na yanke hukuncin cewa shugaba Zelensky bai da ƙudurin ganin an cimma zaman lafiya inda Amurka za ta shiga tsakani."

Sannan ya ƙara da cewa Zelensky "zai iya dawowa idan ya shirya samun zaman lafiya."

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Amurka da Ukraine da kuma Tarayyar Turai ne tun bayan da Donald Trump ya sanar da ƙudurinsa na tattaunawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin lalubo hanyar kawo ƙarshen samamen da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine.

An gudanar da tattaunawa ta farko tsakanin wakilan Amurka da na Rasha a ƙasar Saudiyya a cikin watan Fabarairu.

Sai dai Zelensky da sauran ƙasashen Turai sun bayyana cewa babu wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a cimma game da yaƙin ba tare da an sanya Ukraine da ƙasashen Turai a ciki ba.

admin

admin

Content creator at LTD News. Passionate about delivering high-quality news and stories.

Comments

Leave a Comment

Be the first to comment on this article!
Loading...

Loading next article...

You've read all our articles!

Error loading more articles

loader